Site icon Muryar 'Yanci

Bauchi: Mata 20,000 Ne Suka Ci Gajiyar Tallafin ?angote

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed yace mata 20,000 ne zasu ci gajiyar tallafi na gidauniyar Dangote domin farfado da tattalin arzikinsu dana al’ummar jihar, ta hanyan sana’oi da kuma saye da sayarwa.

Gwamnan yayi wan nan bayani ne a lokacin da Gidauniyar take mika tallafin kudin ga mata masu kananan masana’antu da marasa galihu, a babban zauren wasanni dake daura da kasuwar wunti a fadar Jihar.

Bala yace kudin yakai kimanin naira miliyan dari biyu inda kowace mace zata karbi naira dubu goma,

Sanan ya Kuma yaba ma Gidauniyar tare da Shugaban kamfanin Alhaji Aliko Dangote da tsamo dumbin jama’an Najeriya daga cikin talauci ta hanyan bada tallafi, kana ya ja hankalin wadanda suka samu da suyi amfani dashi ta yadda ya face domin a gudu tare a tsira tare.

Gwamnan ya sake cewa wan nan tallafi babu shakka zai taimaka ma al’umma jihar marasa karfi, Kuma yace rabon kudin tallafin bashi da alaka da siyasa ko sani ko sabo, ko addini ko bangaranci a cikinsa kawai anyi haka ne domin bunkasa tattalin arzikin.

Anashi Jawabin kuwa Shugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote Wanda Shugaban Gidauniyar Inginiya Mansur Ahmad ya wakilce shi a wajen taron yace mata dubu daya ne aka zakulo daga kuwanne karamar hukumomi ashirin na Jihar don aucu gajiyar dubu goma goma na tallafin su fara ja kari.

Ahmad ya Kara da cewa Gidauniyar ta kirkiro wan na.ahirin tun shekaru biyu da suka wuce, don farfado da Mata marasa galihu a dukkanin kanan hukumomin Najeriya baki daya, bugu da kari yace jihohi 13 sun riga sun karbi nasu kason harda Bauchi a halin yanzu.

A ci gaba da Shirin a Karamar hukumar Dass Uwargidan Gwamna Hajiya Aisha Bala Mohammed ta raba ma mata da suka fito daga yankin Dass wan na tallafin na naira dubu goma goma, domin ci gaba da kasuwanci ko fara sana’ar da zai taimaka ma rayuwarsu dana iyalansu baki Daya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Exit mobile version