Babban Kwalejin kimiya da Fasaha ta tarayya dake Jihar Bauchi zata fara koyar da kwasa-kwasai na karatun digiri a fannoni tara 9 har da kerekere da fasaha irin na zamani.
Shugaban hukumar makarantar Arc. Sunusi Waziri Gumau, ya bayyana hakan yayin rantsar da sabbin dalibai zangon karatu na shekarar 2019/2020, Inda aka gudanar da taron ranar Asabar, a babban filin wasa na makarantar.
Arc. Waziri Gumau ya ci gaba da cewa makarantar zata gudanar da kwasa kwasan ne tare da hadin gwiwa da makarantar Jami’ar tunawa da Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchin, don bama dalibai daman cike guraben karatu, tare da samun ilimi mai inganci.
Shugaban makarantar ya jaddada aniyar hukumar makarantar na gudanar da digirin a fannonin kerekere, gwaje gwaje da tsare- tsaren na gidaje da kimiyya, harkokin noma da, ma na fasahar na’ura mai kwakwalwa woto komputa,
kana yace tuni hukumar tantance makarantu da suke koyar da digiri ta amince da wan nan hadaka na karatun digirin, Yace tun kafin yanzu makarantar tana koyar da karatun chanza layin karatu don kwarewar dalibai na hadaka da hukumar makarantar Sojoji dake Jihar Kaduna wato (NDA).
Bugu da kari da yake magana game da sabbin daliban, yace sun dauki dalibai su kimanin dubu 9,910 inda aka rantsar da 9,654 domin fara karatun ba tare da wata matsala ba.
Hakanan Gumau, yaja hankalin daliban dasu sa himma da kwazo ta wajen koyan abin da ya kawo su daga dukkan fadin Nigeria har ma da waje, domin samun ilimi mai ingaci, ya kuma yi godiya ga dukkanin sauran shuwagabani tare malaman makarantar a matakai dabam dabam da kuma iyayen dalibai na kusa da na nesa.
Ya kuma godewa hukumar tara rarar kudin tallafin makarantu na gaba da sakandare wato (Tetfund) da irin gudummuwa mai tsoka, da take bayarwa ta wajen gine-ginen ajujuwa da offisoshin malamai, da tallafin karo ilimi, cikin Najeriya da waje, yace abun a yaba ne.
Bugu da kari, ita ma ana ta jawabin shugaban tsare tsare na hukumar makarantar, (Registrar) Hajiya Rakiya Maleka, tayi gargadi ma sabbin daliban dasu guji shiga cikin abinda babu ruwansu domin a gudu tare a tsira tare, ta fanin samar da ilimi mai nagarta, da samun sakamako mai kyau.
Daliban sunsha rantsuwa fara karatu tare da zimman zama dalibai na gari abin koyi damn tunkaho ga al’umma baki daya.
Daga Adamu Shehu Bauchi

