Site icon Muryar 'Yanci

Bauchi: Kamfanin BUA Ya Bada Gudummuwar Motoci Da Amawali

Gidauniyar Kamfanin BUA ta bawa Jihar Bauchi Motar daukan majinyata guda Uku da amawalin baki, dubu hamsin, don ci gaba da dakile yaduwar annobar mashakon numfashi a dukkan fadin jihar.

A lokacin da yake karbar gudumuwar kayayyakin a gidan gwamnati, a ranar Litinin, Gwamnar Jihar Bala Abdulkadir Mohammed, yace za suyi amfani da kayan ta wajen bada kariya daga daukan chutar da ta addabi duniya korona, da kuma sauran chututuka masu saurin yaduwa a cikin al’umma.

Gwamnan da ya jagoranci kwamitin dakile yaduwar cutar mashakon numfashin a wajen mika kayan, ya jaddada kudirin gwamnati na ganin an kawo karshen wan nan annoba a fadin jihar dama Najeriya baki daya.

Kana yaja hankalin yan’kwamitin da suji tsoron, Allah suyi amfani da kayan kamar yadda aka saba, ta hanyar da ya dace ayi amfanin dasu, yace kar a karkatar dasu don yin wani abu na dabam.

Gwamnan ya kara da cewa, in Allah ya rubuta za a baka, to za abaka, komai daren dadewa, an baba wasu jihohi a baya amma sai yanzu na Bauchi yazu, yace muna godiya kwarai a matsayin al’ummar jihar Bauchi Allah ya saka ma wan nan gidauniya da alheri.

Yayin da yake mika kayan ga gwamnan jihar, Dokta Idi Hong wan da ya wakilci shugaban rukunin kampanin BUA a Najeriya, yace sun kawo kayan ne da nufin bada tasu gudummuwar ga jihar Bauchi, kan yaki da annobar korona.

Kana Hong, ya jaddada manufarsu na inganta rayuwar al’ummar kasan nan, da kuma kara dankon zumunci na kasuwanci da al’ammuran yau da kullun.

Kwamitin dakile yaduwar chutar ta jiha, wanda mataimakin gwamnan Sanata Baba Tela ke jagoranta, sun yaba da irin hobbasa na kampanin BUA da jajircewa ta wajen tallafa ma marasa galihu, tare da yin godiya na musamman a madadin gwamnatin jihar baki daya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Exit mobile version