Cibiyar Hudda da Jama’a ta Kasa ta Yi dashen Itatawa Guda Dari biyu a Makarantar Kimiyya da Fasaha ta gwamnatinta tarayya da Kwalejin Ilimi dake Kangere a Jihar Bauchi, domin kariya daga kwararowar hamada da zaizayar kasa.
Cibiyar tayi hakan ne a wani mataki na bada tasu gudumuwar da kuma taimaka ma Gwamnati ta wajen yaki da wan nan
matsalar zaizayar kasa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Shugaban cibiyar ta kasa Mukhtar Zubairu Suraj yace sunzo Bauchi ne domin gudanar da taron su na Shekarar Shekarar wanda za ayi a karo na farko a Jihar Bauchi da ma yankin arewa maso gabashin kasar
Anasu Jawaban Shugaban Makarantar Kimiyya da Fasaha ta tarayya Arc. Waziri Sanusi Gumau da takwarar sa na Kwalejin Ilimi dake Kangere Adamu Magaji Yumbunga sunce babu shakka cibiyar tayi hangen nesa ta wajen dashen itatuwan, kana sunsha alwashen bama itatuwan kariya domin amfanin al’umma baki daya.
Bugu da kari Shugaban chibiyar na jihar Bauchi, Kabiru Ali Kobi yace taron na Shekarar shekara da za’ayi a Bauchi zai bada damar karfafa dankon zumunci a tsakanin yayan cibiyar da ma sauran Jama’a daga ko’ina a fadin Najeriya
Daga Adamu Shehu Bauchi

