Rundunar Yansandan Jihar Bauchi sun Sami nasarar Chafke Musa Hamza Mai shekaru 22 da haihuwa da Zargin yaudarar Adamu Ibrahim dan shekara 17, inda ya Yanke kansa tare da Kwakule Masa idano a cikin jeji a karamar hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi.
Kakakin Yan’sanda na Jihar Muhammed Wakil shine ya tabbatar ma da manema labarai aukuwar wan nan lamari a garin Bauchi.
Kakakin Yan’sandan ya kara da cewa sunsami rahoton wan nan ta’asa ne biyo bayan jami’an su na karamar hukumar suka Chafke wanda ake Zargin da aikata hakan a unguwar Wake dake karamar hukumar ta Alkaleri. Inda bayan ya yankashi, ya cire kan, ya Kwakule idanun, san nan ya babbaka kan da gangan jikin da wuta, ya kuma birne a rami dabam-dabam
Yaci gaba da cewa a yayin gudanar da bincike dukkanin sassan jikin da Musa Hamza ya birne an ganosu a cikin ramuka kusa da jejin da ya aikata wan nan danyen rashin imani, aka garzaya zuwa babban Asibitin karamar hukumar don tabbatar da mutuwan Adamu Ibrahim a hukumance.
Mohammed Wakil, yayi nuni da cewa ansamu idanun da ya kade na Ibrahim a hannumsa dumu dumu, kuma a cewar Kakakin Wakil, Musa Hamza ya amsa laifinsa, inda yace Bokan shine yace masa ya kawo idanun mutum, domin ya zama mai arziki ba tare da wani bata lokacin ba.
Wakil, yace a cikin makaman da aka samu a hannun sa sun hada da wuka guda daya da mp3 player, takalami na runa guda daya da Kuma fitillar guda daya.
Sa anan kakakin Yan’sandan, yace suna ci gaba da bincike sosai kan wan nan lamari, da zarar sun kammala zasu mika shi gaban kuliya, don Yanke masa hukincin da yada ce da laifin da ya aikata.

