Site icon Muryar 'Yanci

Bauchi: An Dam?e Matar Dake ?oye ‘Yan Bindiga

Rundunar ?an sandan jihar Bauchi sun kama wata mata da ake zargi da baw masu muggan laifuka mafaka sakamakon kama ?arayi biyu da ?an fashi a gidanta.

Kakakin rundunar ?an sandan jihar Bauchi, DSP Mohammed Ahmed Wakili, shine ya bayyana hakan ranar a Alhamis.
Ya ce jami’an rundunar, bayan samun bayanan sirri, sun kama wata Sadiya Mohammed Yaro wacce aka fi sani da Sadiya ?aura, ?ar shekara 28, a unguwar ?ofar Dumi ta garin Bauchi.

A cewarsa, matar ta ba masu laifi mafaka a gidanta dake ?ofar ?umi jim ka?an bayan sun kai hari ofishin Komiti a garin Bauchi. An ji matar ta na?i muryarta tana kirari da yabon ?an daban, tana mai goyon ?ayansu.

Wakili ya ce ?ansanda sun kama masu laifi biyu masu suna; Yakubu Hussaini wanda aka fi sani da Abba Laba, Sai kuma Bashir Ahmad wanda aka fi sani da Bashoo, mai shekaru 23, dukkansu daga ?ofar ?umi, kuma suna cikin sanannu ?an ta’addan da suka addabi jihohin Bauchi, Gombe, Plateau da Kaduna.

Ya ce ?an ta’addan sun tsere daga hannun hukuma a shekar 2019. Ya kara da cewa suna daga cikin wa?anda suka kai harin Ofishin kwamiti a unguwannin Zango da ?ofar ?umi a jihar Bauchi.

Exit mobile version