Daga Adamu Shehu Bauchi
Anshawarci gwamnatin Jihar Bauchi data cetu kafafen watsa labarai mallakar Jihar daga durkushewa domin itace hanyar da talaka ke da damar yin amfani da ita wajen sauraron ayyukan da gwamnati take aiwatarwa a Jihar, tare da amfani da damar yin korafi kan wasu ababen da suka shige masu duhu a gwamnatance.
Shugaban makarantar Jami’ar tarayya dake kashere a Jihar Gombe Parfesa Umar Pate, shi yayi wan nan kiran a lokacin da yake gabatar da kasida mai taken (Matsalolin Kafafen Watsa Labarai da Yadda za a Shawo Kansu a Najeriya). A wurin bikin bude taron makon Yan’jarida reshennjihar na Shekarar 2020 a garin Bauchi
Yace duk gwamnatin da tasa Kafafen Watsa Labarai a cikin hidimar ta to zata ci nasara a ayyukanta saboda a cewarsa kafafen watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen taimaka mamgwamnati don aiwatar da ayyukannta cikin sauki, don haka yace ya Zama ala tilas a kula da gwamnati ta gyara gidajen radio da talabijin na Jihar domin suyi gogayya da takwarorinsu a ko ina.
Shima da yake nashi jawabin shugaban Yan’jarida na jihar kwamared Umar Sa’idu yace suna kokarinsu a kungiyance suga cewa gwamnati tayi hubbasa wajen tallafa ma Yan’jarida da suke aiki tukuru musamman ma a kafafen watsa labarai mallakar Jihar, don Samar da hanyoyin sadarwa ba tare da wata matsala ba.
Ana shi jawabin gwamnan Jihar wanda mataimakin shi Sanata Baba Tela ya wakil ta a wajen taron, yace sunyi nazari sosoi tare da kai ziyara a wadan nan kafafen watsa labarai kana yace sun fahimci akwai gyare gyare na musamman da gwamnati ya kamata tayi su cikin gaggawa don bun kasa su ta yadda a rika jinsu, Kuma su rika gudanar da ayyukansu cikin himma da kwazo.
Sauran masu bayani a wajen taron sun yaba ma Yan’jarida da kokarin sanar da mutanen kan ababen da suke faruwa ko halin da al’umma dama duniya ke ciki baki daya.

