Rahotanni daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) dake Jihar Yusuf Abdullahi, ya koka kan yadda aka samun yawaitar hadurran mota a jihar a cikin watan Nuwamba na wannan shekarar.
Ya ce a cikin watan da ya gabata, mutane a kalla 35 ne suka mutu a wasu hadurran mota a fadin jihar, yayin da dama suka samu muguwar na?asa.
Kwamandan ya bayyana damuwarsa kan lamarin inda ya bayyana cewa: Shaidanun aljanu sun mamaye hanyoyin Bauchi a yan kwanakin nan.
Kwamanda Abdullahi, wanda ke jawabi ga mambobin kungiyar na musamman a ranar Asabar, 4 ga watan Disamba ya ce: Ina baku hakurin fada muku, amma gaskiyar magana ita ce shaidanun aljannu sun mamaye hanyoyinmu a jihar Bauchi.
Lallai muna bukatar mu tashi tsaye mu yi wani abu don kwato hanyoyin. Alamarin ya yi muni sosai, a cikin watan Nuwamba; lamari ne da ake samun mace-mace a kowace rana domin ba a kasa samun mutuwar mutane 35 ba sakamakon hadurra a fadin jihar.
Wannan abin damuwa ne kuma abin tada hankali, dole ne a yi wani abu da sauri.” A cewarsa: A kan hanyar Bauchi zuwa Kano, mun samu hadurran da suka yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 15.
A kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos, wasu motoci sun yi karo da manyan motocin tafiye-tafiye da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15 tare da kone wasu daga cikinsu kurmus.”

