Site icon Muryar 'Yanci

Batanci: Kungiyar Kare Musulmi Ta Bukaci Afenifere Ta Nemi Afuwar Musulmi

?ungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya wato Muric, ta bukaci ?ungiyar kabilar Yarbawa ta Afenifere ta nemi afuwa kan kwatanta Annabi da Sunday Igboho, jagora ?an awaren yarbawa.

Afenifere ta kwatanta gudun hijira da Igboho ya yi zuwa Jamhuriyar Benin da wanda Annabi ya yi daga Makkah zuwa Madina.

A wata sanarwa da ta fitar shugaban ?ungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce kalaman Afenifere ?atanci ne ga addini da Annabi, wanda ba za a lamunta ba.

Jaridar Sahara reporters a Najeriya ce ta soma wallafa wannan ?atanci da Afenifere ta yi, batun da ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta da alla-wadai tsakanin ?an Najeriya.

Exit mobile version