Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi barazanar gurfanar da babbar jamiyyar adawa ta PDP a gaban kotu, bisa zargin bata sunan shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu.
Sakataren yada labaran hukumar Mr Rotimi Lawrence Oyekanmi ne ya bayyana wannan barzana a birnin tarayyar kasar Abuja.
A cewar sa jamiyyar PDP na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da bata sunan shugaban hukumar ta hanyar zargin sa da magudi a zaben da ya gabata da kuma saura tsarin naurar tantance masu zabe ta BVAS da gangan kawai don samun nasarar jamiyyar APC.
Ya ce bayan kiraye-kirayen sallamar shugaban hukumar da PDP ke yi, da kuma maka ta a kotu bisa zargin hada kai da magudi, jamiyyar na kuma ci gaba da bata sunan shugaban hukumar a idanun duniya da angiza yan Najeriya kan su tsane shi ko ma kai masa hari.

