Site icon Muryar 'Yanci

Bashin Dala Miliyan 800 Da Buhari Ya Karbo Daga Bankin Duniya Abin Takaici Ne – Cibiyar Sa-ido

Cibiyar sa-ido kan ayyukan majalisar dokokin Najeriya, CISLAC ta koka kan bashin dala miliyan 800 da gwamnatin kasar ta karbo daga Bankin Duniya, domin rage radadin cire tallafin man fetur.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce yin hakan wani bakon abu ne, saboda idan an daina bayar da tallafin tun a watan Afrilu, to kamata ya yi a mayar da kudaden da gwamnatin ta karbo daga babban bankin duniya.

Shugaban kungiyar ta CISLAC, Awwal Musa Rafsanjani, ya shaida wa BBC cewa a ganinsu, idan aka kar?o bashi kamar yadda doka ta tanada, ya kamata a ce an yi amfani da shi wajen samar da ayyukan da za su amfani ?asa.

“Bashi da aka kar?o lokacin da gwamnati za ta mi?a mulki abin damuwa ne saboda ba a san ma ko gwamnatin da za ta zo, ko za ta amince ta ci gaba da wa?annan tsare-tsare ba.” in ji Rafsanjani.

Shugaban ?ungiyar ya ce sun sha yin kira ga gwamnati game da kar?ar basuka, inda suke nusar da gwamnati cewa akwai hanyoyin da suka fi dacewa da za a iya samun ku?a?en shiga ya zamana ba kowane lokaci za a kar?i bashi ba.

Exit mobile version