Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya yabawa takwararsa na Jihar Ebonyi, David Umahi da ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma Jam’iyya mai mulki ta APC.
Bello Matawalle ya alakanta ficewar Mista Umahi daga PDP ta “rashin jituwa tsakanin ‘ya’yan jamiyyar ta PDP da Gwamnan na Ebonyi.
Gwamnan Zamfaran, wanda dan jam’iyyar PDP ne ya yi wannan jawabin ne ta bakin mai magana da yawunsa, Zailani Bappa a ranar Juma’a a wata takardar sanarwa da ya fitar.
Matwalle ya ?ara da cewa ya gwammace ya jinjinawa Mista Umahi “kan babban matakin da ya dauka a maimakon sukarsa domin mutum na iya zama ne a gidan da ake maraba da shi.”
“Idan wannan rashin jituwar ya cigaba da wanzuwa ba a magance shi ba, jam’iyyar mu ce za ta cigaba da fuskantar matsala a yayin da muke tunkarar zaben 2023,” a cewar Gwamna Matawalle.
“Ina fuskantar kallubalai a baya-bayan nan daga wasu takwarorina na PDP kuma hakan na daure min kai. Misali, gwamnonin PDP na Kudu maso Kudu sun shiga kafafen watsa labarai suna ruruta wutar batun gwal din Zamfara bisa rashin fahimta da karerayi,” inji Gwamna Matawalle.
“Abin mamaki, gwamnatin tarayya ta APC ce ta fito ta bayyana gaskiyar lamarin kan ha?ar gwal din ta kare ni a kan batun. A matsayinsu na ‘yan uwana na PDP, ina tsammanin zasu tuntube ni don jin ta baki na kafin su fara yada maganganu marasa dadi a kafafen watsa labarai,” in ji shi.
Gwamna Matawalle ya yabawa gwamnatin tarayyar Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari bisa goyon bayansa wurin tsara bangaren tattalin arzikin jiharsa don kare amfani da ma’adinan wurin janyo fitintinu a jihar.
“A yau gwamnatin tarayya tana bada lasisi ga kamfanonin da suka cancanta a jihar. Kamfanin da ta saka hannun jari mafi girma mallakin wani dan Najeriya ne daga jihar Anambra. A yanzu, gwamnatin jiha bata da hannu a harkar hakar ma’adinai don kundin tsarin mulki bai bamu dama ba.
“Ina kira ga gwamnonin kudu maso kudu su kauracewa lalaci su tallafawa mutanensu su bude kananan matattun man fetur kamar yadda doka ta basu iko a maimakon yada jita-jita,” in ji Matawalle.

