Sakamakon matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na sauya fasalin wasu takardun kudin kasar, an umarci alummar kasar da su mayar da tsoffin kudaden da za a sauya zuwa banki.
CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari.
Ya ce saboda wannan sabon tsarin yanzu an cire duk wani caji da ake yi a kan kudin da ake kai wa bankuna ba tare da bata lokaci ba, kuma duk yawan kudin.
To sai dai kuma masana tattalin arziki a Najeriya, sun yi tsokaci a kan waadin mayar da tsoffin kudin da za a sauya zuwa banki.

