Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, ya bayyana cewa hatsarin mota bai rintsa da shi ba kamar yadda ake ta rade-radi a kafafen sadarwa na zamani.
Osinbajo ya bayyana cewa sun ci karo da wani hatsari da aka yi ne a hanyarsu ta zuwa filin jirgin sama don haka sai suka tsaya domin taimakawa wadanda lamarin ya ritsa da su.
Ya bayyana cewa jamian tsaronsa da tawagar likitocinsa sun taimaka wajen kwashe mutanen da suka yi hatsarin daga wajen da lamarin ya afku, sannan suka mika su asibitin sojoji.

