Mai Martaba Sarkin Bichi da ke Jihar Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ce ya so a ce yarsa, Zahra ta kammala karatunta kafin ta auri Yusuf, da ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
An dai daura auren Zahra da Yusuf ne ranar Jumaa, 20 ga watan Agustan 2021 a Fadar Sarkin na Bichi bayan Sallar Jumaa.
To sai dai a cikin wata tattaunawarsa da Aminiya, Sarkin ya yi bayani a kan dangantakarsa da yayansa.
Ya ce ya kan shiga tsaka mai wuya a duk lokacin da zai aurar da yayansa saboda shakuwarsa da su.
Ina da kusanci da yayana sosai, saboda aurar da Zahra ma ba karamin tsaka mai wuya ya saka ni ba, amma Alhamudillah.
Karamar yarinya ce, shekararta 20 kacal, kuma tana shekarar karshe ne a jamia inda take karantar Fasahar Zane-zanen gine-gine (Architecture).
Na so a ce ta samu ta kammala karatunta a jamia, sannan ta dan zauna da mu ko da kadan ne, amma ba haka Allah ya tsara ba, kuma ba zamu iya canza ikonSa ba, sai dai kawai mu yi musu fatan alheri, inji shi.
Watakila, Sarkin ya dada shiga damuwar ne kasancewar a farkon shekarar nan ma ya aurar da wata diyar tasa.
To amma fitaccen dan kasuwar kuma basaraken, wanda kuma shine Shugaban kamfanin sadarwa na 9mobile da ma wasu kamfanoni da dama ya ce ya sami natsuwa ne daga wani Hadisin Annabi (S.A.W).

