Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon shugaban hukumar za?e (INEC), Farfesa Attahiru Jega, bai shiga siyasa domin tsayawa takara ba, inda yace sam bashi da shirin neman kujerar shugaban ?asa a 2023.
Jega ya fa?i hakane a wurin wata lakca da yan Kwara suka shirya ranar Asabar, yace bai fa?awa kowa yana da sha’awar neman mu?amin shugaban ?asa ba.
“Ban fa?a wa kowa cewa inada da sha’awar tsayawa takarar shugaban ?asa ba, jita-jita ce da ra?e-ra?in kafafen watsa labarai.”
“Eh, gaskiya ne na yi rijista da jam’iyyar siyasa, saboda na yanke hukuncin cewa ba zan tsaya ina zuba ido ba kawai, zan bada tawa gudummuwar a siyasar Najeriya.” “Akwai lokacin komai amma a yanzun bani da shirin takara.
Ni musulmi ne, na yi imani da Allah kuma nasan cewa ba abinda ya gagari Allah, saboda haka na barwa Allah komai.” Farfesa Jega ya ?ara da cewa mafi yawan mutanen dake cikin gwamnati a yanzun ba su san hanyar warware ?alubalen ?asar nan ba. Saboda haka, tsohon shugaban INEC ya yi kira ga yan Najeriya su tuhumi yan siyasa kan duk abinda ke faruwa.
Tun a shekarar 2019, tsohon shugaban hukumar za?e kuma kwararre a ilimin siyasa ya bayyana shigarsa jam’iyyar PRP. Hakanan kuma a watan Satumba, 2021, Jega yana daga cikin wa?anda aka bayyana a sabuwar jam’iyyar da zata ceto Najeriya daga halin da ta shiga.

