Site icon Muryar 'Yanci

Badakalar Emefiele: Kotu Ta Bada Umarnin A Saki Sarkin Hausawan Legas Da Matarsa

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja, ta umurci hukumar tsaro ta farin kaya SSS ta saki Sarkin Hausawan Lagos Aminu Yaro da uwargidan sa Sa’adatu yaro, wadanda aka kama akalla makonni biyu da su ka gabata bisa zargin su da hannu a badakalar dakataccen gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emfeile.

A wani hukunci na daban da aka yanke a ranar Talatar da ta gabata, an bayyana ci-gaba da tsare Aminu Yaro da matar sa Sa’adatu Yaro a matsayin wani yunkuri na take hakkin su na Bil-Adama.

Mai shari’a Edward Okpe ya bada umurnin, bayan ya saurari bahasin lauyoyin ma’auratan, wadanda su ka hada da Labi Lawal da Adedayo Adedeji bayan an karanto korafin da su ka gabatar wa kotun.

Lauyoyin dai sun shigar da karar ne a ranar 18 ga watan Yuli, akalla mako guda bayan an kama Aminu Yaro da matar sa, kuma karar ta hada da hukumar tsaro ta SSS da ofishin Atoni janar na tarayya a tsayin wadanda ake kara.

Da ya ke yanke hukuncin, alkalin ya bada umurnin wucin-gadi na a saki mutanen da ke tsare a hannun hukumar SSS a Abuja, ko kuma duk inda su ke har sai yadda shari’ar ta kaya.
Mai shari’a Okpe, ya kuma hana hukumar tsaro ta SSS yunkurin kamawa ko kuma muzguna wa ma’auratan, sannan a karshe ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Yuli domin ci-gaba da saurare.

Rahotanni sun ce, hukumar tsaron ta kama Sarkin Hausawan Lago kuma shugaban majalisar Sarakuna Aminu Yaro da uwargidan sa ne a gidan sa da ke Abuja a ranar 12 ga watan Yuli.

Wata majiya ta ce, kamen ba ya rasa nasaba da binciken da dakataccen gwamnan babban Bankin Nijeriya Godwin Emefeile ke fuskanta a kan badakalar canjin kudade.

Idan dai ba amanta ba, a baya shugabannin al’ummomin Arewa da ke Lagos sun bukaci a gaggauta sakin Aminu Yaro, yayin da rahotanni ke cewa alakar da ke tsakanin shi da Emefeile ba ta da bambanci da wadda ke tsakanin dakataccen gwamnan babban bankin da sauran Sarakuna da masu ruwa da tsaki a Nijeriya da ma duniya baki daya.

A karar da lauyoyin shi su ka gabatar, an kama Aminu Yaro ne a ranar 12 ga watan Yuli kafin daga bisani aka hada da matar sa.

Alauyoyin sun cigaba da cewa, a ranar 10 ga watan Yuli hukumar SS ta gayyaci Aminu Yaro zuwa Ofishin ta da ke Abuja, inda a nan ne ya fahimci akwai yiwuwar matar sa ta gurfana a gaban kotu a kan wasu tuhume-tuhume biyu.

Daga cikin zarge-zargen dai, ana tuhumar Aminu Yaro ne tare da kamfanin M.A.Y Fine Fragrance, yayin da ake tuhumar Sa’adatu Yaro tare da Kamfanin Tsami Resoureces Limited, bayan lauyouyin shi sun gano cewa hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kan shi, amma ba ta gano wani laifi da ake zargin shi da aikatawa ba.

Lauyoyin sun cigaba da cewa, gayyatar da hukumar SSS ta yi wa Aminu Yaro a ranar ta same shi cikin uzuri, don haka ya bukaci jagoran tawagar lauyoyin sa Joseph Daudu ya rubuta wa hukumar bukatar sanya wani lokaci, amma duk da haka, a ranar ne jami’an hukumar su ka yi wa gidan sa da ke Abuja kawanya tun da misalin karfe 5 na asubahi.

Sun ce da shigar jami’an hukumar SSS cikin gidan, ba tare da bata lokaci ba su ka yi awon gaba da basaraken da kuma matar sa zuwa ofishin su, inda har yanzu su ke tsare da su.

Sai dai majiyoyi sun ce, har yanzu ba a samu ko daya daga cikin laifuffukan da ake zargin shi da aikatawa ba, kuma maimakon a gurfanar da shi a gaban kotu, sai hukumar ta buge da amfani da kafafen yada labarai wajen jifar ma’auratan da zarge-zarge marasa tushe.

A hukuncin da kotun ta yanke dai, ta bada umurnin a saki Aminu Yaro, tare da sharadin zai gabatar da kan sa domin sauraren shari’a bayan ya samu ‘yanci.
Haka kuma, lauyoyin sun bukaci a gaggauta sakin Sa’adatu Yaro a matsayin matar aure, domin kauce wa duk wani yanayi da zai jefa ‘ya’yan ta cikin mawuyacin hali, sai dai majiyoyi na cewa har yanzu hukumar SSS ba ta mutunta umurnin kotun ba.

Exit mobile version