Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya ce babu wani ?angare na mutane ko addini ko ?abila da ya isa ya yi babakere ga shugabancin Najeriya.
Gwamnan ya fa?i haka ne a lokacin da shugaban ?ungiyar Kiristoci ta Najeriya Rev, Ayokunle Samson Olasupo ya kai masa ziyara fadar gwamnatin Sokoto, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin gwamnan na Sokoto ta bayyana.
Tambuwal ya ce “shugabancin Najeriya na taimakon juna ne saboda haka, Najeriya ta kowa ce kuma babu wanda zai kori wani daga ?asar, akwai bu?atar ci gaba da zama tare domin ci gaban ?asa.”
A nasa ?angaren shugaban ?ungiyar CAN, Olasupo ya ce ya kai ziyara Sokoto ne domin tattaunawa da Sarkin Musulmi da kuma mutanen Sokoto domin gano bakin zaren yadda za a magance ?alubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Ya kuma jajantawa alummar jihar kan mutanen da aka kashe a hare-haren ?an bindiga tare da yin kira ga zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista.

