Site icon Muryar 'Yanci

Babu Wanda Ya Isa Ya Ta?a Mutumin Kudu A Jigawa – Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, ya kwantar da hankalin ‘yan kudancin Najeriya mazauna jiharsa cewa shirye yake da kare rayukansu da dukiyoyinsu daga dukkanin wata barazana.

Gwamnan ya bada wannan tabbaci ne ranar Asabar yayinda ya karbi bakuncin gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, a jihar Jigawa a ziyarar sada zumunci da ya kawo mishi.

Gwamna Badaru ya gayyaci takwaransa na Ebonyi ne domin kaddamar da wata hanya a karamar hukumar Babura, Mahaifar Gwamna Badaru.

Badaru ya yi amfani da daman domin jawabi ga Inyamuran da suka fita kwansu da kwarkwatansu domin tarban gwamnan na Ebonyi.

“Muna godiya mutan kudu na zaman lafiyansu a Jigawa tare da mu, kuma muna son bayyanawa kowa cewa ku kwantar da hankalinku a Jigawa da sauran jihohin Arewa,”

“Ku fadawa ‘yan siyasan dake son kawo rashin jituwa kasar nan cewa ba zasuyi nasara ba saboda babu wanda zai tayar da hankalin ‘yan kudu a Arewa.”

Gwamnan ya ce gwamnati ba zata zuba ido a cutar da wani a Jigawa ba.

A jawabinsa Gwamna Umahi ya godewa gwamnonin Arewa bisa kokarin samar da zaman lafiya a Najeriya.

Exit mobile version