Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i ya bayyanawa yan kasuwar jiharsa su cigaba da amfani da tsaffin kudadensu kuma ya basu tabbacin babu abinda zai faru.
A wani taro da yan kasuwa ranar Talata, El-Rufa’i ya ce idan aka zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, matsayin shugaban kasa, zai yi watsi da dokar sauya fasalin Naira.
El-Rufa’i ya baiwa yan kasuwan tabbacin cewa duk wanda ya rasa kudinsa ya kamasu da alhaki amma yana musu alkawarin babu abinda zai samu kudinsu.
“Ku daina canza kudadenku kuma ku fadawa kowa ya daina kai kudinsa banki. Idan kun sayar da wani abu, ku ajiye tsaffin kudadenku. Ku daina cewa sabbin kudi kadai zaku karba saboda kasuwancinku zai tsaya kuma haka suke so.”
“Ku fadawa kowa a Kaduna mai tsaffin kudi su kashe kudinsu. Ku fadawa kowane dan kasuwa ya kashe kudinsa.” Nasir el-Rufai, Uba Sani, da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na muku alkawarin cewa idan aka zabemu, za’a canza wannan doka kuma kowa zai samu isasshen lokaci don sauya kudinsa.”

