Shugaban Namibia Hage Geingob ya ce ya yi jinkirin kar?ar allurar rigakafin korona saboda likitocinsa sun ba shi shawarar kada ya bari a yi masa allurar AstraZeneca da aka ba ?asar.
Ya ce nemi bu?atar rigakafin Johnson & Johnson daga Afirka ta Kudu da ke makwabtaka da Namibia.
Sun gwada ni kuma sun ce saboda shekaru na da kuma rashin lafiyar hawan jini ya fi dace wa na kar?i allurar Johnson & Johnson ko kuma Pfizer.
Korona na ?ara bazuwa a Namibia, inda sama da mutum 1,000 suka kamu da cutar cikin mako biyu.
Mutum sama da 100,000 aka yi wa allurar rigakafin korona a ?asar.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce duk da ana samun rahotannin samun matsalar toshewar jini bayan kar?ar AstraZeneca, ta ce amfaninta ya fi hatsarinta.

