Mai magana da yawun shugaban ?asa Malam Garba Shehu, ya ce Gimba Yau kumo da hukumar ya?i da cin hanci ta ICPC ke nema ruwa a jallo yanzu ba surikin shugaba Buhari ba ne.
A cikin wata sanarwa da Garba Shehun ya fitar a ranar Jummaa ya ce auren da ke tsakanin jamiin da ake zargin da ?iyar shugaba Buhari ya jima da mutuwa.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Garba Shehu na cewa koda ma auren bai mutu ba shugaba Buhari kamar yadda kowa ya san shi ba zai bayar da kariya ga duk wani mai laifi ba.
Tun a shekara ta 2016 ne dai aka ?aura auren da ke tsakanin ?iyar shugaba Buharin da kuma wanda ICPC ke nema. Sai dai Garba Shehu bai fa?i zahirin lokaci da shekarar da auren ya mutu ba.
ICPC dai na zargin Gimba Yau Kumo ne da zambar ku?a?en da suka kai Dala miliyan 65 kuma hukumar ta ce jamiin ya gudu.

