Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed yasha alwashin kawo karshen rikicin albashin ma’aikatan Jihar a cikin Watan Maris na wan nan Shekarar ta 2021
Gwamnan yayi wan nan furucin ne a daidai lokacin da yake ganawa da shuwagabannin kananan hukumomi da na ma’aikatun gwamnati
a matakai dabam dabam.
Bala Abdulkadir yace ya kamata a yanzu asaka maganan albashin ya zama abin da anwuce shi tuntuni a dukkan fadin jihar, kuma zamuyi hakan da yaddan Allah.
“Mu bamu rike albashin kowa ba, duk abin da mukeyi, bai wuce mu tabbatar da ganin mutane basu sha wahala ba babu gaira babu dalili, yayin da muke kokarin samar da tsarin biyan albashin ta hanyar tantance sunayen ma’aikata na asali na masu aikin gwaamnatin Jihar nan, ba haka za’ayi ta tafiya ba, dole ne muyi aiki da ku don samun maslaha” Gwamnan yace.
Kana yaja hankalin shuwagabbani da cewa karsu manta su zababu ne na al’umma, daboda haka su tsaya suyi Mutanen aiki tukuru, yace duk da musan cewa jinka daya baya daukan daki sai an hada large da karfi san nan aci nasara
Bala ya nusar da shuwagabbani da su rika aiki kafada da kafada da jami’an tsaro a mataki kananan hukomomin su domin dakile wata barna da kuma masu yada kayan baya ko yan bindigan daji da masu garkuwa da mutane
Gwamna Bala ya kara cewa munsan kune manya a kananan hukumomi, muna baku kudi ko mai kashinsa, ku rika rage kashe kashen kudade wadan da basu da alaka da mutane kai tsaye, dole mu chanza tsarin shugabanci a Jihar Bauchi.
Muna sa ran baku yanci karbar kudaden ku Kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya, domin ku gudanar da aiki ma al’umman kananan hukomomi, don rage nauyi ma gwamnatin, kuma zai bamu daman rage wasu matsaloli wa gwamnatin Jihar.
Daga Adamu Shehu Bauchi

