Site icon Muryar 'Yanci

Babu Ranar Da Ba A Yi Mana Fya?e – Matan Da Aka Ceto Daga Zamfara

Wasu daga cikin ‘yan mata 26 da akayi garkuwa dasu a kauyen dan aji dake karamar hukumar faskari dake jihar katsina sun bayyana yadda ‘yan bindiga suka ci zarafin su, ta hanyar fyade da duka a kullum.

?aya daga cikin ‘yan matan mai kimanin shekaru 35 cikin alhini da takaici take bayyana cewar an duke su tare da yi masu fyade a lokacin da suke hannun yan ta’addan. ”Tace mun kwashe kimanin kwanaki uku muna tafiya a kasa inda cikin dare kawai muke tafiya a yayinda idan gari ya waye sai su ajiye mu cikin daji har sai yamma tayi kamin mu cigaba da tafiya cikin dajin.

Tafiyar da mukayi cikin dajin nan yana daya daga cikin abinda baza mu taba mantawa dashi ba. Domin munga tashin hankali a kauyen dan aji daje karamar hukumar faskari Wanda bamu taba ganin irinsa ba. Bayan an karkashe tsofaffin mutanen kauyen tare sa sace kayayyakin abincine aka tafi damu cikin dajin nan muna ta tafiya har saida karfin mu ya kare.

Washe garin ranar suka ware manya cikin mu da masu ciki guda 8, inda sukaiwa sauran fyade iya iyawar su. Mu kuwa da ba aimana fyaden ba cikin dare haka za suyi ta dukan mu tare da yi mana barazanar kisa. A haka dai suka samu dafa masu shinkafa da wake sai manja da gishir, shi muke ci inda idan dare yayi kuma muke dafa masu tuwo da miya…

Wannan kusan shine karo na farko da ake samun labarin halin Wanda akayi Garkuwa dasu suke shiga a hannun yan ta’addan duk da gwamnatin jihar katsina da zamfara sunyi shiru akan lamarin. Sai dai gwamnan jihar zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewar tattaunawa da sukayi da yan ta’addan ya janyo sakin matan nan 26 ba tare da biyan kudin fansa ba inda matan nan suka karyata gwamnan domin wakilan su sun bayyana cewar an biya kudaden fansa kamin a sako iyalansu.

Kamar yadda Muhammad Lawal Amadu ya bayyana wa wakilin mu, yace yan ta’addan sun kawo hari ne kauyen mu na dan aji dake karamar hukumar faskarin jihar katsina a ranar 13 ga watan oktaba da misalin karfe 5:23 na yamma su kimanin 500 a babura dauke da manyan makamai. Sun shiga gida gida suka sace kayayyakin abinci da sauran abubuan anfani kala kala. Sun hallaka mutane 16 a kauyen nan take inda suka dauki matan kauyen namu kimanin su 24 tare da kona wurare da dama. Sun farfasa shagunan mutane sun diba kayayyakin masarufi da sauran kayayyakin anfani na yau da kullum.

Matan da suka yi garkuwa dasu a kauyen mu sun shafe kwanaki 23 a hannun su kamin mu biya kudaden fansa, amman ba gwamnatin jihar zamfara bace ta amso iyalan mu.

Da farko sun bukaci mu biya su kudin fansa inda muka harhada kudi naira miliyan biyu da dubu dari daya (2.1m) sukace mu ajiye a kasar wata bishiya dake cikin dajin dake tsakanin jihar katsina da zamfara.

Bayan sun amshi kudin sukace kudaden sunyi kadan kuma baza su sake iyalan mu ba sai mun cika dubu dari hudu domin kudin sukai jimillar miliyan biyu da rabi. Nan ma dai muka kara yin karo karo muka kai masu.
Nan ma suka ce kudaden baza su ishe su ba nan ma dai bayan kwanaki kadan muka kara masu miliyan da da dubu dari bakwai (1.7m).

Bayan mun basu kimani naira miliyan shida da dubu dari shida (6.6m)ne suka sako iyalan mu, dawowar su keda wuya gwamnatin jihar zamfara ta gayyace mu domin jin ta bakin iyalan mu amma kuma duk da bayanan da mukayi masu suka fito suke gayawa duniya sune suka kubutar da iyalan mu.

Shima daya daga cikin mazauna kauyen dan aji mai suna Abdulkadir Musa ya bayyana cewar saida ya siyar da duk abinda ya mallaka kamin ya samu biyan kudin fansar iyalansa guda hudu acikin matan da akayi garkuwa dasu.

Na siyar da Gona na da kayan abincin da noma domin samun iyalina da sarkuwata da akai garkuwa dasu cikin mata 26 da aka sace a kauyen dan aji.

Shima a nasa jawabin gwamanan jihar katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewar zasu cigaba da sulhu da yan ta’addan domin ganin samun sauran mutanen da suke hannun yan ta’addan

Kuna ganin sulhu da yan ta’addan zai kawo karshen matsalar garkuwa da mutane a yankin arewacin kasar nan???

Exit mobile version