Site icon Muryar 'Yanci

Babu Nasara Ko Guda Da Buhari Ya Samu A Mulki – PDP

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta mayar da martani kan nasarorin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi i?irarin ta samu a 2021, tana mai cewa galibinsu ‘?arya ne’

PDP ta kira nasarorin da ministan ya?a labarai Alhaji Lai Mohammed ya bayyana a ranar Alhamis a “matsayin ?arya daga gwamnatin da ta gaza.”

“I?irarin nasara da gwamnatin APC ta yi babban abin dariya ne na shekara.”

A wani taron manema labarai da ya gudanar, ministan ya?a labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce duk da an fuskanci ?alubale na tsaro da ta tattalin arziki a shekarar 2021, amma gwamnatin Buhari ta samu nasara a fannoni da dama.

Ministan ya bayyana nasarorin gwamnatinsu ta APC a fannin tsaro da tattalin arziki da ayyukan ci gaba. Kuma ya takaita nasarorin APC ne kawai a 2021.

Sai dai a wata sanarwa mai taken “I?irarin nasarorin gwamnatin tarayya a 2021, ?arya ne kawai,” PDP ta mayar da martani kamar haka:

Game da nasarorin tsaro da APC ta bayyana yawan maya?a da aka kashe 1,000 a arewa maso gabas da ?an bindiga a arewa maso gabashi 427 da kuma yawan maya?an Boko Haram 22,000 da suka mi?a wuya, PDP ta ce “gwamnatin da ake kashe jama’arta bai kamata ta fito tana murna da yabon kanta ba duk da gazawarta yayin da ?an ta’adda suka addabi al’umma.”

Ta fuskar tattalin arzki, PDP ta ce ta bar wa APC tattalin arzikin da ya kai dala biliyan 550 mafi girma a Afirka a 2015, amma ?asar ta koma cibiyar talauci a duniya saboda rashin iya gudanar da mulki da rashawa da ri?on sakainar kashi na gwamnatin APC.

PDP ta ce a 2015 ana bin Najeriya bashin dala biliyan 7.3 amma a yanzu cikin shekara shida bashin ya kai sama da dala biliyan 38.

Jam’iyyar hamayyar ta kuma ce, gwamnatin APC ba ta da abin cewa, saboda a ?ar?ashin mulkin jam’iyyar darajar naira ta fa?i kan dalar Amurka daga N198 a 2015 zuwa N500 a yanzu. Kuma farashin kayan masarufi sun yi tashin gauron zabi.

Ta kuma ce ta?o farashin fetur inda ta ce daga N87 a 2015 yanzu ana sayarwa kan N165.

PDC ta ce abin dariya ne gwamnatin APC ta yi i?irarin cewa tana ya?i da rashawa, bayan kuma ta zama matattarar ?an siyasa masu kashi gindi. Jam’iyyar hamayyar ta kuma ce wannan ne ya sa APC ta gaza hukunta jami’ai da shugabanninta da ake tuhuma.

“Shi ya sa ba ta da amsa kan rahoton da ya banka?o yadda shugabannin APC suka wawuri naira tiriliyan 25 daga hukumomin gwamnati,” kamar yadda PDP ta yi i?irari.

Babbar jam’iyyar mai hamayya a Najeriya ta ce “abin takaici ne gwamnatin APC ta fito tana lissafa ayyukan more rayuwa a matsayin nasarori wa?anda a takarda kawai suke tare da ?o?arin aiwatar da ayyukan da gwamnatin PDP ta yi.

“PDP ta ?alubalanci gwamnatin APC ta fito ta bayyana wani muhimmin aiki da ta tsara, ta fara ta kuma kammala a cikin shekaru shida da suka wuce,” in ji babbar jam’iyyar adawar.

Exit mobile version