Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jamiyyar PDP, Sule Lamido, ya caccaki ayyukan jamiyyar APC a kasar nan, inda ya bayyana su a matsayin bigi bagiro.
Yayin da yake bayyana ayyukan gwamnatin APC kawo yanzu, Lamido ya bayyana jamiyya mai mulki a matsayin jamiyya juya wacce ba ta iya samar da kyakkyawan shugabanci ga kasar nan ba a tsawon lokaci da ta ?auka akan mulki.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai ranar Talata, a birnin tarayya Abuja.
Lami?o ya yi nuni da cewa jamiyyar mai mulki ita ce ke tafiyar da mulki amma ba ta da karfin kawo canjin da yan Najeriya ke bukata, ta gaza ta kowane fanni.
Abin da su (APC) suke cewa PDP kazanta ce amma suna farautar mambobinmu su zo su gina jamiyyarsu. APC da ke daukar yayan PDP zuwa cikinsu cin rashawa ne. Babu nagari a APC. Jamiyyar ta rashawa ce matuka.
Da yake magana kan taron gangamin jamiyyar PDP da aka kammala da kuma damar da jamiyyar za ta samu a zaben 2023, Lamido ya bayyana fatan samun nasara ga jamiyyarsa, inda ya kara da cewa sakamakon taron na nuna hangen ci gaba ga kasar.

