Tsohuwar jaruma Finafinan Hausa Zakiyya Ibrahim Abdullahi, ta yi kira ga Yan jarida da su rinka gudanar da aikin su a bisa doron aikin jarida, a matsayin su na wadanda Allah ya dora musu nauyin fadakar da jamaa da wayar musu da kai, a kan abubuwan da su ke faruwa a duniya.
Jarumar ta yi wannan kiran ne, a lokacin da ta ke hira da wakilin jaridar Dimokuradiyya, a kan labarin da wata jarida mai suna Damagaram Post ta yi, in da ta ce, wai tana neman mijin aure.
Jarumar ta Kara da cewar Sam babu wani lokaci da na taba yin hira da wani dan jarida na fada masa ina neman mijin aure, saboda haka ban san a ina suka samo labarin na su ba, kuma suka alakanta ni da shi. Inji ta.
Idan ina neman mijin aure ba zuwa Soshiyal Midiya zan yi ba na rinka tallan kaina ba, kuma idan tallan kai ne ai mu a matsayin mu na yan fim duniya ta gama sanin mu. Don haka labarin da suka yada ba gaskiya ba ne, don har na so na dauki mataki na sharia a kan su, saboda bata mini sunan da suka yi.

