Jamiyyar APC ta yi abin da Bahaushe ke cewa ka fi mai kora sosawa, yayin da ta nuna jin ciwon zafafan kalaman da Sanata Ali Ndume ya yi wa Shugaban ?asa Bola Tinubu.
APC ta yi masa raddin cewa kasa samun damar ganawar da Ndume ya yi da Tinubu ba zai ta?a zama dalili ko hujjar cewa wasu sun kange shugaban ?asar daga ganawa da yan Najeriya ba.
Sakataren Ya?a Labarai na APC na ?asa, Felix Morka ne ya yi wa Ndume wannan raddi, wanda ke ?unshe cikin sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar, a Abuja.
A cikin makon ne Sanata Ndume ya yi ?orafin cewa wasu yan ba-ni-na-iya sun kange Tinubu daga ganin jamaa.
Ndume wanda ya ce ?am?are ?ananan hukumomi daga jikin gwamnonin jihohi ta hanyar samar masu yancin cin gashin kai, shi ne ka?ai babbar nasarar da ya samu tun bayan hawan sa mulki, duk da haka ya ?ara da cewa amma fa Tinubu ?in bai ma san irin ?alubalen da ?asar nan ke fama da su ba.
Wannan ?a?atu na baya-bayan nan da Sanata Ali Ndume ya yi, wanda ke wakiltar Barno ta Kudu, kuma Bulaliyar Majalisar Dattawa ta 10, wanda ya ce wai Shugaban ?asa bai san halin matsalolin da ?asar nan ke ciki ba, sun yi tsauri, kuma babu dalilin da zai feso wannan magana.
A matsayin sa na sanata, Ndume ya na da dandamalin da zai yi magana kan wasu batutuwan da suka shafi alfanun ?asar nan.
Kuma ya na da damar ganawa da dukkan jamiai Da hukumomin gwamnatin tarayya. Cewar Kakakin Ya?a Labarai na APC.
Morka ya ce abin damuwa ne tabbas idan Ndume ya yi ?o?arin ganin Shugaban ?asa, amma abin ya gagara.
To amma kuma hakan ba daidai ba ne da ya ce wai an kange Shugaban ?asa. Kuma kasa ganawa da Tinubu ba dalili ko hujja ba ne da sanatan zai ce an kange Shugaban ?asa daga sanin halin da ?asar nan ke ciki.
Ya ce Shugaban ?asa a ko da yaushe ya na cikin shaanin alamurran ayyukan ?asar nan wa?anda ya maida hankali a kan su, kuma saboda su ?in ne ma aka za?e shi.
Daga nan ya ci gaba da lissafin wasu muhimman ayyukan da ya ce Tinubu ya gudanar da wa?anda ya zartas da kuma wa?anda ke gaban sa a yanzu.

