Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun ce hasashen da Asusun Lamuni na Duniya IMF ya yi cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a kasar a karshen bana, romon baka ne kawai.
Masanan sun ce wannan ba abu ne mai yiwuwa ba matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba.
Cikin wata hira da ya yi da BBC, Dakta Murtala Abdullahi Kwara, shugaban sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar Umaru Musa ‘Yar-Aduwa da ke Katsina, ya ce ko shakka babu hasashen da ya zo daga masana, to amma abin mamaki idan aka kalli wani abin to tabbas za a ga babu wani dalilin fadarsa sai don a farantawa wasu bangare na gwamnati rai ko kuma wasu sun yi rawa ya kamata a yaba musu.
Ya ce, Idan aka yi laakari da yadda farashin wasu manyan kaya ke tashi a kullum ya za a yi a gasgata hasashen IMF?.
Masanin tattalin arzikin, ya ce, Tun da farko ma hasashen Asusun Lamunin cewa ya yi farashin kaya ya tashi da kashi 33 cikin 100 a yanzu, to wannan ba gaskiya ba ne, sannan kuma ta ina za a yar da da cewa farashin zai sauka kashi 24 cikin 100 bayan ba a hakikance yadda farashin ma ke tashi.
Matsaloli biyu a Najeriya na tashin farashin dala duk da yanzu gwamnati na kokarin daidaita bangaren da kuma tashin farashin mai, sune zasu sa duk wani hasashe da IMF zai yi muke kallonsa a matsayin shaci fadi ne kawai wanda bashi da wata makama.In ji shi.
Dakta Murtala Abdullahi Kwara,ya ce duk wanda ke rayuwa a Najeriya ba sai na fada masa cewa matakan da gwamnatin kasar ke dauka na tattalin arziki, kara tsunduma talakan kasar cikin wahala suke.
Ya ce, Duk wani tsari da aka fito dashi a Najeriya wanda IMF ke bayar da shawara a kansu, wannene ya yi tasiri? Misali cire tallafin mai wanda shi ne ya haifar da balain da Najeriya ta tsinci kanta ciki a yanzu, haka tsare tsaren tsuke bakin aljihu da gwamnati ta fito da su me ya canja?
Masanin tattalin arzikin ya ce idan aka bi tarihi babu wata kasa guda a duniya da ta bi shawarwarin IMF da yanzu ta ke zaune lafiya.
Idan gwamnatin Najeriya ta na son a samu raguwar hauhawar farashin kaya a kasar ta ta fito ta yi tsarin da mutane za su samu mai cikin sauki, sannan a bangaren dala kuma, ya kamata gwamnati ta fito da wasu tsare tsare masu karfi na nan take da za a magance matsalar. In ji shi.

