Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin Kano ta musanta zargin da ake yawo dashi na cewar akwai wani yunkurin sauke shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Muhuyi magaji Rimin Gado daga kan mukaminsa.
Gwamnatin ta Kano ta ce a iya saninta babu wata matsala makamanciyyar haka da ake yadawa tsakanin gwamnati da shugaban hukumar.
A zantawar da aka yi dashi Kwamishinan ya?a labarai na Jihar Kano Muhammad Garba yace haka suma suka wayi gari suka ga wannan labari a kafafen yada labarai na zamani.
“Amma ina tabbatar muku da cewar babu wata matsala dake tsakanin gwamnatin Ganduje da Muhuyi Magaji Rimin Gado Shugaban Hukumar ya?i da cin hanci da rashawa na jihar”
Amma a nashi bangaren Magaji Rimin Gado a wata tattaunawa da wani gidan Rediyo ya yi dashi a Kano ya bayyana cewar yana aikin shine tsakani da Allah kuma a shirye yake ayi dukkanin wani bincike da za’a a kanshi.

