Site icon Muryar 'Yanci

Babbar Nasarar Najeriya Shine Samun Buhari A Matsayin Shugaban Kasa – Sarkin Daura

Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Farouk Umar Farou ya bayyana cewar ko shakka babu Najeriya ta yi sa’a da dacewa wajen samun Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin jagora a irin wannan lokaci, wanda wannan na matsayin babbar nasara ga ?asar.

Mai Martaba Sarkin ya ?ara da cewa ba domin Shugaba Muhammadu Buhari ne ke a kan mulki ba a yanzu, da ‘yan Najeriya sun shiga cikin wani irin mawuyacin hali abin kwatance a duniya.

Basaraken ya ce abubuwa “da sun kasance da wahala matuka” idan da a ce ba Buhari ba ne yake jan ragamar mulkin kasar, tun daga kan sha’anin tsaro da walwalar Jama’ar kasa baki ?aya.

Mai Martaba Faruok Umar Farouk ya yi wadannan kalamai ne a ranar Juma’a, 23 ga watan Yuli, lokacin da shugaban kasar ya ziyarce shi a fadarsa da ke Daura, jihar Kastina domin gaisuwar Sallah.

“Zuwanka Daura ya nuna kyawawan halayenka wanda muke matukar alfahari da shi. “Ina iya baka tabbacin cewa maza, mata, yara, ‘yan kasuwa da masu sana’ar hannu a koyaushe suna farin cikin karbar ka kuma zasu yi muka addu’a.

“Yau ba ranar jawabai bane illa ranar godiya. Mun samu albarkatu sosai a matsayinmu na al’umma saboda kai ne shugaban ?asar. Ka kawo daukaka ga yankinmu. “A matsayinmu na al’umma, mun amfana sosai da yawan zirga-zirgar mutane da kungiyoyi da ke zuwa don taimaka mana a nan. Mun san saboda kai ne.

“Najeriya ta yi sa’ar samunka a wannan lokaci. Ba wai ina fadan hakan ne don in faranta maka rai ba, amma da ba ka kasance a kan karagar mulki ba da hakan zai yi wuya. Ina shakka idan za mu kasance a nan a yau.”

Mai Martaba Sarkin ya ce dole ne shugaban kasar ya ci gaba da mai da hankali kan samun sakamako, musamman wajen kare kasar, da dawo da martabar ta kamar yadda aka sani tun farko.

Exit mobile version