Labarin dake shigo mana yanzu haka na bayyana cewar tsohon abokin siyasar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Rufai Hanga ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki cikin gaggawa.
Kamar yadda ya shaida, a halin da ake ciki jamiyyar APC ba ta da wani tasiri don haka bai ga amfanin bata lokacin sa da cigaba da zama cikinta ba.
Hanga wanda babban ginshiki ne na jamiyyar, amma yanzu ya duba ya ga babu mamora don haka ya cika wa rigarsa iska.
Hanga wanda shine shugaban jam’iyyar CPC na farko, ya sanar da jaridar The Independent cewa har yanzu bai shiga wata jamiyyar ba.
CPC ce tsohuwar jamiyyar shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin su yi maja da ACN da sauran jamiyyu su hada jamiyyar APC. A cewar Hanga, duk da ya yi aiki tukuru wurin gina jamiyyar APC, ba zai zauna yana gani jamiyyar ta rushe yayin da yake cikinta ba.
Eh duk da na bar jamiyyar APC, har yanzu ban sanar da jamiyyar da na koma ba. Amma na bar jamiyyar kuma ina ganin abubuwan da suke yi yasu-yasu.

