Site icon Muryar 'Yanci

Babban Lauya Ya Shigar Da Kara A Cire Sunan Najeriya Daga Kasashen Musulmi

A watan da ya gabata ne wani lauya mai suna Malcom Omirhobo a Najeriya, ya shigar da kara domin neman cire kasar daga cikin jerin kasashen musulmin duniya.

Lauyan mai rajin kare ‘yancin dan adam, ya shigar da Gwamnatin tarayya kara yana neman kotu ta haramta wa Najeriya cigaba da kasancewa mamba a kungiyar kasashen musulmai ta duniya wato OIC (Organisation of Islamic Countries)

Lauyan mai suna Malcom Omirhobo ya nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kuma haramta wa duka jihohi 36 na Najeriya da Abuja daga alakanta kansu da wani addini ko nuna fifiko kan wani addini ko bin tsarin wani addini a hukumance a jihohinsu musamman a yankin kudu.

Lauyan ya kara da cewa Najeriya kasa ce ta kowa da kowa wacce ke dauke da mutane fiye da miliyan 200 daki bin addinai da al’adu daban-daban don haka zamewar Najeriya a matsayin mamba a kungiyar kasashen musulmai ya saba wa dokar kasa, sannan tamkar nuna wa duniya ne cewa Najeriya kasar musulmai ne.

A cewarsa lauyan ya nemi kotu ta haramta wa Najeriya cigaba da kasancewa a OIC, ko bayar da wani tallafi ko gudunmuwa daga baitul malin kasar zuwa kungiyar ta OIC.

Exit mobile version