Site icon Muryar 'Yanci

Babban Burina Yanzu Shi Ne Aure – Gwarzuwar Musaba?ar Alkur’ani

Daga Adamu Shehu Bauchi

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar gwarzuwar musaba?ar karatun Alkur’ani mai girma da aka yi a Jihar ‘yar shekara ashirin da haihuwa Haulatu Aminu daga jihar Zamfara a bangaren mata ta bayyana aniyarta ta burin samun mijin aure na gari, bayan nasarar da ta samu.

Da take wa manema labarai ?arin haske kan nasarar da ta samu a karshen gasar da ta gudana karo na 36 a filin wasa na tunawa da Abubakar Tafawa Balewa dake garin Bauchi, Gwarzuwar shekarar tace karatu da jajircewa da Addu’oi gun Allahu Subahanahu wata’ala kan abin da mutum yasa a gabanshi shine sirrin samum nasarar ta.

“Iyaye na su suka biya mini kudin karatu tare da bani karfin gwiwa da babban gudunmuwa mai tsoka, da kuma Malamai na da suka bani ilimi har na kawo wannan matsayin babu abun da zan ce masu sai godiya da ba zai misaltu ba a rayuwata, hakika Ina alfahari dasu” Inji Haulatu.

“A yanzu ban da wani buri da ya wuce in samu mijin aure na gari, in shiga daga ciki”, tare da nuna farin cikin ta da murmushi.

Kana daga karshe Haulatu da Gwarzon shikara na bangaren maza daga Jihar Borno sun karbi kyautar naira miliyan Uku N3m kowannen su, da kuma shirin wakiltar Najeriya a gasar karatun Alqurani mai tsarki na duniya da za’a gudanar nan bada dadewa ba.

Har-ila yau Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammad da ta dauki nauyin shirin tun daga fako har karshe ta bada kyatutuka masu nauyi ga duk wanda ya samu halartar shiga cikin gasar ta bana

Exit mobile version