“Babban burin da nake dashi a rayuwata yanzu shine Allah ya taimakeni in bar harkar fim lafiya, in samu wata sana’a wadda tafi ta, inyi kyakkyawar rayuwa yadda ko na mutu ba zan bar wa ‘ya’yana abin fadi ba”.
Kalaman fitaccen ?an wasan Finafinan Hausa Adam Abdullahi kenan wanda aka fi sani da Adam Zango a yayin tattaunawar da gidan Rediyon BBC Hausa ya yi dashi kan tarihin rayuwar shi.
Adam Zango ya kara da cewar sana’ar Fim ta yi mishi komai a rayuwa, ya samu daukaka wanda bai taba tunanin zai samu ba, duk da tarin kalubale da ya fuskanta a rayuwarshi.
Jarumin ya cigaba da cewar babban abin da ya jawo shi cikin harkar fim shine ganin irin yadda marigayi Rabilu Musa ke nishadantar da jama’a da barkwanci da kuma yadda jarumi Sha’aibu Lawan Kumurci ke taka rawa a matsayin mugu a fim, inda ya bayyana cewar rawar da yafi bukatar takawa kenan a fim fitowa a matsayin Mugu.

