Site icon Muryar 'Yanci

Ba Za Mu Lamunci Maimaita Yakin Basasa A Najeriya Ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin siyasa akan su mayar da hankalinsu don tabbatar da babbar manufar raya bu?atun kasa, yana cewa “mu ?an Najeriya ne, kuma da ikon Allah za mu cigaba da kasancewa ?an Najeriya, sannan Najeriya za ta ci gaba da kasancewa ?asa daya.”

Shugaba Buhari wanda ya fadi hakan a ranar Talata yayin ?ar?ar ba?uncin tsohon shugaban tsohuwar jam’iyyar CPC a fadarsa, ya ce ya lura sha’awa da ?o?arin bun?asa rayuwar ?an Najeriya bai gushe a zu?atan mutane ba, yana mai kira da su sake jajircewa.

Shugaban ya ?ara da cewa bai kamata a maimaita son kan da ya yi dalilin asarar rayuka kusan miliyan ?aya daga shekarar 1967 zuwa 1970 ba.

Buhari yana wannan magana ne da ala?antata da ya?in basasar ?asar na wancan lokaci.

Ya ce ya kamata kuma a yi duk abun da ya kamata wajen ganin haka bai sake faruwa ba, in da ya ?ara da cewa an samar da CPC ne akan gimshi?in kishin ?asa da amana dangane da ha?in kan Najeriya.

Exit mobile version