Shugaban ?ungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, shine ya bayyana haka a wani sa?o da ya fitar ta bakin daraktan ya?a labaransa ranar Asabar –
A ranar Jumu’a data gabata ne, jami’an tsaro suka gano gawarwakin ?alibai uku daga cikin wa?anda aka sace a jami’ar a wani ?auye dake kusa da makarantar ?ungiyar gwamnonin arewa tayi Allah wadai da kisan ?aliban jami’ar Greenfield da Yan bi?diga suka yi.
Shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Plaateau, Simon Lalong, ya bayyana lamarin da tsantsar jahilci da mugunta, yace ba zasu bar lamarin ya tafi hakanan ba.
Lalaong ya fa?i haka ne a wani jawabi da daraktan ya?a labaransa, Dr. Makut Macham, ya fitar ranar Asabar a Jos, babban birnin jihar Plateau. Shugaban gwamnonin yace babu wani uzuri da za’a yi ma kisan ?alibi wanda ba ruwansa, kawai yana karatu ne domin ya bauta ma ?asa nan gaba.
Ya kuma ?ara da cewa ?ungiyarsu zata cigaba da ha?a kai da gwamnatin tarayya wajen gano hanyoyin da za’a magance matsalar satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci musamman a makarantun yankin arewa.
A ranar jumu’a aka gano gawar ?alibai uku daga cikin ?aliban jami’ar Greenfield da aka sace, a wani ?auye wanda yake kusa da makarantar. Yan bindigan sun sace ?ali?ai a makarantar jami’ar Greenfield dake ?auyen Kasarmi, kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ?aramar hukumar Chukun ranar Talata.
A wani labarin kuma Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki Cibiyar inganta addinin musulunci (ICICE) ta bayyana cewa an samu 1.3 biliyan daga cikin 3.15 biliyan da ake nema don kara fadada masallacin An-Noor. Shugaban cibiyar Dr. Kabir Kabo, shine ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja , kuma yace za’a fara aikin bada jimawa ba.

