Fadar Shugaban ?asa ta bayyana cewa Najeriya ba za ta fallasa masu ?aukar nauyin yan taadda ba.
Kakakin Ya?a Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana haka a lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na Channels, ranar Litinin a Abuja.
Adesina ya ce maimakon a fito ana fallasa su ko a kunyata ta su, gwamnati ta maida hankali ne wajen tabbatar da cewa an gurfanar da su, an hukunta su.
Adesina na magana ne a kan wasu yan Najeriya shida da ?asar UAE ta lissafa a cikin jerin mutum 38 da ta ce su na ?aukar nauyin yan taadda.
Najeriya ba za ta fallasa su ko ta kunyata su kowa ya gan su ya san su a yanzu ba. Maimakon haka, ta maida hankali ne a kan ganin an hukunta su.
Kuma tun lokacin da UAE ta fito da bayanin, Ministan Sharia na Najeriya ya yi magana ya ce za a gaggauta tuhumar su da yanke masu hukunci.
Saboda haka mai yiwuwa yanzu bincike ya na matakin EFCC. Ko kuma ba mamaki ya na hannun Hukumar Le?en Asiri ta NIA. Inji Adesina.
Da aka ta?o masa batun shin ko Buhari zai sake kinkimo bashi a Taron Shugabannin ?asashe na Majalisar ?inkin Duniya, sai Adesina ya ce ai taron ba na neman bashi ba ne.
Ba taron neman bashi ba ne. Amma dai wasu shugabannin kan ke?e su tattauna hul?o?i a tsakanin ?asashen su. Kuma bashin da Shugaba Buhari ke ciwowa a yanzu ai ana yin ayyukan raya ?asa ne da su. Sa?anin Gwamnatin baya, wadda idan an ciwo bashin, a cikin aljifan su su ke danna ma?udan ku?a?en. Cewar Adesina.

