Alamu na nuna cewa da yawa daga cikin ?aliban jami’ar Bayero dake Birnin Kano BUK ba za su koma karatu a ranar 18 ga Janairu ba kamar yadda hukumar gudanarwar jami’ar ta bayar da sanarwa ba.
Kwana ?aya da sanarwar janye yajin aiki na tsawon wata tara da ?ungiyar malaman jami’o’in ?asar nan ta yi, da yawan ?aliban jami’o’i sun nuna rashin shirinsu na komawa makarantar a lokacin da aka sanar.
“Ban jima da samun gurbin karatu na digiri na biyu a bangare nazari kan sadarwa ba. Amma sam bana tsammanin dalibai sun shiryawa cigaba da karatu haka da wuri.” In ji wani mai suna Alameen Usman Abubakar.
Abubakar ya cigaba da cewa; “Kamata ya yi ace hukumar gudanarwar ta kammala yin rijista kafin 18 ga Janairu.”
Ya bukaci jami’ar da ta ?ara lokacin yin rijistar zuwa watan Fabrairu don ?alibai su samu damar shiryawa kan lokaci da samun zarafin tunkarar karatun.
Ya bukaci jami’ar da ta ?ara lokacin yin rijistar zuwa watan Fabrairu domin sauran ?alibai su samu damar shiryawa kan lokaci.
Wani ?alibi mai suna Aminu Muhammad na tsangayar nazarin zamantakewa (Sociology) ya bayyana dalilansa da cewa: “Lahadin da ta wuce ne ma na iya samun shiga shafin yanar gizo na makarantar domin yin rijista wanda har yanzu ake yi.”
Ya cigaba da cewa “Na gama biyan duk wasu ku?a?e amma har yanzu ban samu gurbi a jami’ar ba.” Aminu ya yi ?orafin cewa zai yi wahala ace shi ya samu damar kammala rijistarsa kafin 18 ga Janairu.
Hasiya Abubakar, ?aliba mai nazarin biochemistry cewa ta yi, “Dawowa karatun nan ya zo mana babu tsammani duk ?alibai sun gaji da zaman gida.”

