Site icon Muryar 'Yanci

Ba Mu Da Ala?a Da Gayyatar Da Majalisar Wakilai Ta Yi Wa Buhari – Sanatoci

Majalisar Dattawa a ranar Laraba sun nesanta kansu daga gayyatar da ‘?an majalisar wakilai suka yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, don ya zo ya yi bayani kan ta’azzarar rashin tsaro a fa?in ?asar nan.

Wannan ya zo ne lokacin da mataimakin shugaban sanatoci, Ovie Omo-Agege, ya ce hakan ya sa?awa kundin doka sannan kuma ya sauka daga turba da tsarin kowacce irin majalisa ta gayyaci shugaban ?asa ya gurfana a gabanta.

Shi ma Shugaban kwamitin Sanatoci kan ya?a labarai da hul?a da jama’a, Sanata Ajibola Basiru (Osun ta tsakiya) ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa Sanatoci ba su da ala?a ko ka?an da gayyatar shugaban ?asar da majalisar wakilai ta yi.

Ya ce tunda Sanatoci basu gayyaci Shugaban ?asar ba, ba su so a jefasu cikin sar?a?iyar ko shugaban ?asar zai amsa gayyatar ko akasin haka.

“Ba nine mai magana da yawun Sanatocin Najeriya ba. Amma babu sa hannun sanatoci kan gayyatar shugaban ?asa ya zo ya yi bayani akan sha’anin tsaron ?asa. “Ina tsammanin dukkan wata bu?atar gayyata ko kiran shugaban ?asa za’a tura ta zuwa majalisar wakilai.

“Majalisun mu sun sha ban ban da juna. Wannan ne yasa tsarinmu da dokokin mu suka bambanta, hakan ne yasa ake bu?atar ha?in kai a tsakaninmu don zartar da doka ko kudiri.” “Akan wannan batun, babu wani batun ha?aka tsakanin mu.

Abin da ake da shi shine ha?in kan majalisar wakilai ka?ai.”
“Kuma na yarda majalisar wakilai zata iya fa?a muku dalilin da yasa aka mi?a gayyatar da kuma abin da zai faru akai” “A iya sanin Sanatoci, ba mu gayyaci shugaban ?asa ba, kuma ba ma son mu saka kanmu cikin wannan sar?akiyar akan ko shugaban ?asa zai halarta ko akasin haka.”

“A iya sanina, ban da wata masaniyar ha?aka tsakanin mu da majalisar zartarwa”.

Dangane da maganar Abubakar Malami, Ministan shari’a, da ya ce majalisar zartarwa bata da ikon gayyatar shugaban ?asa ya ce.; “Ni masanin doka ne, ban karanta abin da Malami yace ba, idan na karanta, kuma naga ya shafi sanatocin Najeriya zan maida martani.
Ba zan iya maida martani kan ra?e ra?i ba.

Exit mobile version