Site icon Muryar 'Yanci

Ba Fulani Ka?ai Ke Aikata Ta’addanci A Najeriya Ba – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaj Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya soki kudin goro da ake yi wa dukkan fulani saboda hare haren da wasu mutane da ake ikirarin yan kabilar ne ke yi, a yankin Arewacin Najeriya.

Da ya ke magana yayin taro da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, MACBAN, a ranar Juma’a a Abuja 29 ga watan Janairu, Sultan wanda shine shugaban kwamitin amintattu na MACBAN, ya ce duk da cew akwai wasu fulani da ke laifi kamar yadda ake samu a wasu kabilun, ba daidai bane a rika yiwu dukkan fulani kallon bata gari.

A yayin da ya amince akwai fulani cikin galibin masu garkuwa da mutane, Sultan din ya ce ba su kadai suke shirya garkuwar ba domin suna samun taimakon wasu kabilun.

“Nima asalina bafulatani ne amma ni mutumin kirki ne. Ni ba mai laifi bane. Wadanda ke aikata laifi suna da yawa a sasan kasar. Ba daidai bane a wari wata kabila daya ana danganta ta da wani laifi.
“Misali, idan sun karbi N10m ina zaka je ka kashe kudin a daji? Kudin cikin gari zai koma, na fada wa Sufetan Yan sanda cewa ba wai munce Fulani ba su garkuwa da mutane bane kamar yadda sakataren Miyetti Allah ya fadi, bakwai zuwa takwas cikin wadanda ake kamawa da garkuwa Fulani ne amma hakan baya nufin duk wani Baffillatani mai laifi ne.

“Ya zama dole mu hada hannu wuri guda don kawo karshen wannan matsalar. Za mu tuntubi shugaban kasa ya yi wa makwabtan mu na kasashen Afirka ta Yamma inda muke da Fulani kamar Senegal, Nijar Guinea da Mali domin mafi yawancin bata garin su kan shigo daga wasu kasashen ne suyi laifi su koma.”

Exit mobile version