Site icon Muryar 'Yanci

Ayyukan Ta’addanci Sun Ragu Matuka A Najeriya – Rahoto

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar an samu raguwar ayyukan ta’addanci a Najeriya musamman a shekarar da ta gabata ta 2021.

Rahoton da Hukumar da ke sanya ido kan Ayyukan Ta’addanci a duniya wato Global Terrorism Index ta fitar, ya nuna cewa an samu saukin hare-hare ta’addanci a Najeriya da akalla kashi 72 cikin 100 a shekarar da ta gabata.

Rahoton ya bayyana cewar wannan dalilin ya sanya a yanzu Najeriya ta koma matsayin ta shida daga ta uku a tsakanin kasashen da su ka fi fama da matsalar ta’addanci a duniya.

Rahoton ya ?ara da cewar ayyukan ta’addanci kungiyar Boko Haram ya ragu matuka tun bayan mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a shekarar bara.

Hakazalika rahoton ya bayyana cewar dakarun sojin Najeriya na samun nasara a ya?in da suke yi da kungiyoyin ‘yan bindiga wadanda ke addabar yankin arewa maso yammacin kasar.

Exit mobile version