Site icon Muryar 'Yanci

Auren Gata: Hisbah Ta Ware Wa ‘Yan Jarida Gurbi 50 A Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi wa ’yan jarida albishir ?in gurbi 50 a auren gata da za ta gudanar nan ba da jimawa ba.

Yayin ganawa da manema labarai, Shugaban Hisba na Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce matakin ya biyo bayan nasarar da hukumar ta samu a auren gatan 1,800 da ta gudanar a baya.

“Mun bai wa ’yan jarida da sauran ma’aikatan kafafen ya?a labarai da ke sha’awar shiga tsarin auren gurabe 50.

“Haka kuma mun shirya ha?awa da masu aiki a bangaren shari’a, da ma’aikatan lafiya domin tabbatar da an shigar da rukunin mutane iri-iri a tsarin,” in ji Daurawa

Ya kuma ce makasudin ?ir?iro tsarin auren shi ne kawar da ba?ala a tsakanin matasa. Baya ga haka kuma ha?a aure tsakanin matasa na yaukaka ala?a tsakanin al’umma da hukumar.

Daurawa ya kuma ce Hisbar ta ha?a guiwa da manyan makarantu da ke jihar, domin samar da makarantar bayar da horo da kuma koyar da dabarun ayyukan da suka shafi aikin hukumar, domin ?abba?a ?o?arinsu na inganta al’adu da addini a jihar su kuma tafi daidai da zamani.

Exit mobile version