Tun bayan auren Fitacciyar Jarumar shirin Kwana Casain Rahama M K wato Fulani Matar Bawa Maikada, a watan daya gabata mutane suke ta tofa Albarkacin bakin su a game da auren nata da Kuma makomar ta a cikin harkar fim Musamman shirin Kwana Casain.
To sai dai Jarumar ta yi magana da Jaridar Dimukaradiyya a Karo na farko inda ta tabbatar da zata ci gaba da fitowa a harkar fim ba ma shirin Kwana Casain ba har ma da sauran finafinai da ta ke yi.
Jarumar ta bayyana cewar Ai ita harkar fim kamar aikin Gwamnati ne ko kasuwanci da Matan aure su ke yi don haka zan ci gaba da yin fim tun da sanaa ta ce da na ke yi na ke samun kudi saboda auren na ba zai hana ni fitowa a fim ba.
Daga karshe ta yi godiya ga dukkan mutanen da su ka yi Mata fatan alheri a game da auren da ta yi.

