Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban majalisar amintattu a PDP, Adolphus Wabara ya nuna za a iya fito da Mazi Nnamdi Kanu idan Atiku da Jam’iyyar PDP suka lashe za?e.
Sanata Adolphus Wabara yana cewa Atiku Abubakar ya ba shi tabbacin cewa shugaban Yan IPOB zai samu yanci a gwamnatinsa. A cikin kwanaki 100 na farko da Atiku Abubakar zai yi a ofis idan ya zama shugaban kasa, zai saki Nnamdi Kanu ba tare da yanke masa wani sharadi ba.
Adolphus Wabara ya shaidawa Duniya wannan ne yayin da ya ke tallata dan takaran shugaban kasar na jamiyyar PDP a wajen kamfe a garin Umuahia babban birnin Jihar Abia.
Tsohon shugaban majalisar ya ce maganar a maida Ibo saniyar ware a Najeriya, zai zama tarihi da zarar Atiku Abubakar Wazirin Adamawa ya shiga fadar Aso Rock.

