Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?an takarar shugaban Najeriya ?ar?ashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jagoranci wata zanga-zangar lumana da jam’iyyarsa ta shirya a Abuja domin nuna adawa da sakamakon za?en shugaban ?asar na 2023.
Shugaban jam’iyyar na ?asa Iyorchia Ayu, da ?an takarar mataimakin shugaban ?asa gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta, da kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal na daga cikin wa?anda suka halarci zanga-zangar.
Ita dai jam’iyyar PDP na zargin an tafka magu?i a za?en wanda ya gudana a ranar 25 ga watan Fabarairu, wanda hukumar za?en Najeriya -INEC ta sanar da ?an takarar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe za?en.
Baya ga PDP, ita ma jam’iyyar Labour wadda Peter Obi ya yi takara a ?ar?ashin ta, ta soki sakamakon za?en inda ta sha alwashin ?alubalantar sa a kotu.
Sun yi zargin cewa babu adalci a za?en wanda aka yi amfani da na’urar BVAS.

