Site icon Muryar 'Yanci

Atiku Ya Cancanci Tsayawa Takarar Shugabancin Kasa – Gwamnatin Adamawa

Rahotanni daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar Gwamnatin jihar a ranar 27 ga watan Yuli, ta shaidawa kotun tarayya da ke Abuja cewa Atiku Abubakar ya cancanta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a 2023.

An ruwaito cewa attoni janar na jihar Adamawa, Afraimu Jingi, yayin gabatarwa kotu hujojinsa ya shaidawa Mai Shari’a Inyang Ekwo cewa yana son a gwamutsa shari’ar da wata kungiya ta shigar kan Atiku da wasu mutum uku.

Kungiyar ta EMA cikin kara mai lamba FHC/ABJ/CS/177/2019, ta yi karar Atiku, Jam’iyyar PDP da Hukumar zabe mai zaman kanta, (INEC) da attoni janar na kasa, AGF, Abubakar Malami.

A cewar rahoto, EMA na ?alubalantar cacantar Atiku na yin takarar shugaban kasa a kan cewa ba a Nigeria aka haife shi ba, shi bakon haure ne daga jamhuriyar Kamaru.

An ruwaito cewa kungiyar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba idan aka yi la’akari da sashi na 25(1) &(2) and 131(a) na kundin tsarin mulki da yanayin haihuwansa.

Amma Jingi, ta hannun lauyansa, Cif L.D. Nzadon, a kara mai dauke da kwanan watar ranar 26 ga watan Afrilu da aka shigar ranar 24 ga watan Yunin 2021 ya bukaci a gwamutse batutuwan wuri daya.

Lauyan ya bayyana lamarin a matsayin ‘batu ne da mutanen kasa ke bibiya kuma ya dace a yi biyyaya a kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) a batun zaben shugaban kasar Nigeria.

Inda ya bayyana cewar Atiku, wanda aka shigar da karar saboda shi, dan kasa ne daga jihar Adamawa wanda aka zaba a matsayi gwamnan jihar a 1999 kuma ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007.

Exit mobile version