Mai ba shugaban ?asa shawara na musamman kan harkokin ya?a labarai, Femi Adesina ya ce tsohon shugaban ?asa Atiku Abubakar na cikin wa?an da suka ?ata Najeriya wanda har abada ‘yan Najeriya ba za su manta ba.
A martani da ya mayar kan magan-ganun da ya yi kwanan nan, Adesina ya ce “Atiku ba zai iya tsame hannunsa daga yadda Najeria ta zama ba.”
Atiku, wanda shine ?an takarar shugaban kasa ?arkashin jam’iyyar PDP a za?en 2019, ya ce a ?ar?ashin mulkin Buhari Najeriya ta kama hanyar lalacewa.
Yana mai cewa, Buhari bashi da ?warewar da zai mulki ?asar, kuma dole ne ‘yan Najeriya su taimaka ma gwamnatin don su tseratar da kansu.
Atiku ya kuma soki wasu kudirorin Buhari, yana mai cewa yawaitar marasa aikin yi a Najeriya ya wuce tunani, kuma tabbas wannan shine silar matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki.
Amma lokacin da yake maida masa martani a shirin gidan Talabijin na ‘Channels TV’, Adesina yace: “Idan zaka iya tunawa lokacin da ake shirye-shiryen za?en 2015, ya yin da APC ke tallata ‘yan takarar ta, a lokacin adadin da Buhari ya yi aiki dashi na marasa aikin yi a ?asar ya kai miliyan 30, kuma mafiyawancin su matasa ne, ya kuma yi al?awarin gwamnatinsa za ta yi wani abu akai.”
“Wannan a wancan lokacin kenan 2014/2015. Kada kazama kamar kifin rijiya mana wanda ya fito yanzun. Dama can akwai rashin aiki a ?asa.”
Tsohon mataimakin Shugaban ?asa ne shi na tsawon shekaru takwas, kuma yanzun yana ?angaren hamayya, ba zamu ?auki duk abinda ya fa?a gaskiya ne ba.
Babban abin da zamu tambayeshi shine: “Lokacin mulkinsu da shi da tsohon shugaban ?asa Olusegun Obasanjo, ina suka kai Najeriya, kuma ina suka barta?” inji Adesina.
Adesina ya kara da cewa, naga wasu bidiyoyi a kafar sada zumunta shi da kansa yana cewa mutane sun amshi ayyukan tiriliyoyi a mulkinsu amma basu yi komai ba.
Adesina ya kara da cewa, ba zai yuwu ya cire kansa ba, ya koma gefe yana yanke hukunci. Ya yi nashi na tsawon shekaru takwas kuma sun bar mulki inda suka barshi “Ba zai yuwu ya koma gefe ya wanke kansa ba shi ka?ai.

