Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar malaman jamia na reshen jamiar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta yi kira ga shugabannin jamiar da su karbe digirorin da suka ba Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar ASUU ta cin ma matsaya cewa a raba Malam Nasir El-Rufai da shaidar karatun da ya samu a jamiar. Hakan na zuwa ne bayan sabanin da aka samu tsakanin mai girma gwamnan na jihar Kaduna da shugabannin jamiar ABU Zaria game da batun wani fili.
Kungiyar ta ce abubuwan da gwamnan na Kaduna yake yi, sun ci karo da koyarwa da tarbiyar da ya samu daga wannan babbar jamia mai dadadden tarihi.
ASUU ta cin ma wannan mataki bayan zaman da tayi a Samaru Zaria a ranar Laraba, 2 ga watan Maris 2022, a karkashin jagorancin Farfesa Haruna Jibril. Sabon shugaban ASUU da sakatarensa a ABU Zaria, Haruna Jibril da Husseini Abdullahi su ka sa hannu a takardar da aka fitar bayan wannan zaman.
Takardar tana cewa malaman jamiar sun tattauna a kan batun yunkurin gwamna Nasir El-Rufai na karbe filin ABU da karfi da yaji, duk da kotu ta hana shi.

