Jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriya ta zargi wani gwamna mai ci a yanzu da ?aukan nauyin ?an bindiga, da zama jagoransu wanda ke tsara musu yadda zasu tafiyar da ayyukan su na ta’addanci musanman a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, wato Jihohin Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Kebbi da Jihar Sokoto.
Duk da cewa APC bata ambaci sunansa ba, amma a cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ta yi ikirarin cewa ‘binciken sirrin’ da ta yi ya nuna cewa wani gwamna daga Arewa maso Yamma yana hada kai da ?ata gari don tada fitina a yankin.
Wannan zargin na zuwa ne bayan sace ‘yan makarantar sakandare da wasu da ake zargin yan ta’addan kungiyar Boko Haram ne suka yi a karshen makon jiya.
Duk da ma?udan ku?a?en da ake kashewa a kan tsaro, har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza kawo karshen hare-haren yan bindiga. Arewa maso yamma yanki ne cikin yankuna shida na Najeriya da ke da jihohi bakwai.
Jihohin su ne Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara. Jami’yar APC ke mulki a biyar daga cikinsu yayin da PDP ke mulkin jihohi biyu.
Da ta ke ?orafi game da ta?ar?arwar harkar tsaro a kasar, APC ta yi kira ga hukumomin tsaron kasar su dauki matakin gaggawa.
“Rahotonnin binciken sirri da muka yi ya danganta ?aya daga cikin gwamnonin arewa maso yamma da ha?a kai da ?aukan nauyin barnar da hare-hare da ?an bindiga ke yi a yankin.
Ba zan bada cikakken bayani ba saboda batun sirri ne wannan. “Don haka, muna kira ga hukumomin tsaro da abin ya rataya a kansu suyi bincike don tabbatar da sahihancinsa. Ran ?an adam ba abin wasa bane ko abinda za a siyasantar da shi,” a cewar mataimakin kakakin APC na kasa, Yekini Nabena.

